An kama sojan da ya kashe wani matashi mai zanga-zangar yunwa a garin Zariya

0 165

Rundunar soji ta kama sojan da ya kashe wani matashi mai zanga-zangar yunwa a garin Zariyan Jihar Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce sojan ya kashe mai zanga-zangar ne a lokacin da yake kokarin tarwatsa wasu bata gari.

Nwachukwu, ya ce an kama sojan wanda ya yi harbin da nufin gargadin masu zanga-zangar amma ya harsashi ya samu matashin.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa dakarun soji a jiya, sun samu kiran gaggawa cewa “wasu bata gari sun taru a Samaru, suna ƙone tayoyi a kan hanya tare da jifan jami’an tsaro da duwatsu.

Ya ce nan take sojoji suka isa wajen domin tarwatsa gungun matasan tare da tabbatar da dokar hana fita da gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya. Ya kara da cewa an yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, wanda manyan sojojin suka halarta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: