Gwamnatin Tarayya ta tura wa talakawa miliyan 4.3 kudaden tallafi domin rage musu radadin rayuwa

0 132

Gwamnatin Tarayya ta ce ta aike wa talakawan kasar miliyan 4.3 kudaden tallafi ta asusun ajiyarsu na banki domin rage musu radadin rayuwa.

Ministan Kudi, Wale Edun ne, ya bayyana haka tare da alkawarin ci gaba da tallafa wa mutane miliyan guda a kowane wata.

Ministan, ya ce shirin zai ci gaba da tafiya har zuwa lokacin da za su rika bai wa mutane miliyan guda tallafi kowane mako ko makonni biyu.

Edun, ya kuma kara da cewar gwamnati na daukar kwararan matakai wajen ganin ta inganta harkar noma da samar da abinci domin ganin an rage dogara ga kasashen ketare wajen shigo da abinci.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kasar ke ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa, al’amarin da ya tilasta musu gudanar da zanga-zanga domin nuna bacin ransu kan radadin da suke ciki. 

Sai dai zanga-zangar ta haifar da rudani tare da halin rashin tabbas a kasar, tsakanin shugabanni da kuma talakawan da suke mulka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: