An kama wani dan acaba mai shekaru 35 bisa yunkurin sace wasu dalibai 2 a jihar Katsina.

0 257

A wani Labarin kuma, Rundunar Hukumar Tsaro ta Civil Defence ta kama wani Dan Achaba mai shekaru 35 bisa yunkurin sace wasu Dalibai 2 a jihar Katsina.

An kama Mutumin mai suna Abdurrashid Mohammed, wanda yake zaune a unguwar Jangefe ta jihar, tare da mikashi ga Ofishin hukumar dake Katsina.

Da yake zantawa da manema labarai, a birnin Katsina Kakakin hukumar DSC Mohammed Abdara, ya ce wani Jami’in su ne wanda ya kai ziyara wata Makaranta, ya kama mutumin ne a lokacin da yake kokarin sace Yaran daga Makaranta.

A cewarsa, Mahaifin Yaran ne ya fahimci abinda mutumin yake kokarin yi, inda ya fadawa Jami’in nasu abinda yake faruwa domin kama mutumin.

Mista Abdara, ya bukaci Iyaye da hukumomin Makaranta su rika sanya Idanu kan yayansu biyo bayan abinda yake faruwa na matsalar tsaro a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: