Majalisar Karamar Hukumar Buji ta Jihar Jigawa ta hana yara kanana fita kiwon dabbobi a yankin

0 282

Majalisar Karamar Hukumar Buji ta nan Jihar Jigawa ta hana Yara Kanana fita Kiwon Dabbobi a yankin.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Karamar hukumar Alhaji Ali Safiyanu, ya rabawa manema labarai, ciki harda Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN.

Sanarwar ta ce Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Abdullahi Suleiman, ya sanar da dokar dakatarwar a lokacin da yake ganawa da Kwamatin Manoma da Makiyaya na yankin.

Ali Safiyanu, ya rawaito wurin da Shugaban Karamar hukumar ya bukaci Kwamatin Sashen Aikin Gona na Majalisar ya tabbatar da cewa ya gabatar da rahoton sa domin hukunta mutanen da aka samu suna cinye Makiyaya da Burtalai a yankin.

Shugaban Sashen Aikin Gona na Karamar Hukumar Buji Alhaji Hassan Abdullahi Garkuwa, ya ce kwamatin sa ya gano mutanen da suke cinye Makiyaya da Burtalai da kuma mutanen da suke Noma filayen da aka ware a yankin.

Jami’in Yada Labaran, ya ce Mambobin Kwamatin sun kunshi Kansiloli da Masu sarautun gargajiya da Manoma da kuma Mambobin Kungiyar Miyatti Allah.

Leave a Reply

%d bloggers like this: