Fiye da gonaki 95 wanda darajarsu ta kai Naira biliyan 1.5 ambaliyar ruwa ta lalata a jihar Kano

0 103

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano ta ce gonaki 95 wanda darajarsu ta kai Naira biliyan 1.5, ambaliyar ruwa ta lalata a Kananan Hukumomi takwas na jihar.

Sakataren zartarwa na hukumar, Dr Sale Jili, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran na Kasa a Kano.

Dakta Sale Jili ya ce hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, ta yi hasashen ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 25 na jihar saboda tsammanin ruwan sama mai karfi.

Ya ce kimanin mutane 26 ambaliyar ta kashe, tare da rushe gidaje dubu 2,026 da kuma lalata, gonakan shinkafa 95 kazalika mutane 19 sun jikkata sakamakon ambaliyar a jihar.

Mista Jili ya bayyana sunayen kananan hukumomin da abin ya shafa da suka hada da Bunkure, Minjibir, Tarauni, Doguwa, Rano, Ungogo, Tudun Wada da Tsanyawa.

Mista Jili ya ce hukumar ta tura jami’ai zuwa karamar hukumar Tudun Wada wanda bala’in ya yi wa illa don tantance barnar don samar da cikakkun bayanai.

Ya ce Gwamnatin Jiha tare da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya sun kafawa ‘Yan Gudun Hijira, sansani tare da basu katifu da kayan kwanciya ga wanda ambaliyar ruwa ta shafa da za su iya daukar mutane sama da 700.

Leave a Reply

%d bloggers like this: