An kashe mutum 12 yayin sannan 6 sun samu raunika biyo bayan wani hari da yan Bindiga suka kai jihar Katsina

0 111

Kimanin mutane 12 ne aka kashe, yayin da kuma wasu 6 suka samu raunika biyo bayan wani hari da yan Bindiga suka kai a gundumar Duba ta karamar hukumar Batsari a Jihar Katsina.

Gidan Talabijin na Channels Tv ya rawaito cewa yan bindigar su kimanin 300 sun kai harin ne dauke da Makamai a jiya da Daddare.

Kakakin rundunar Yan Sandan Jihar Katsina SP Gambo Isah, shine ya tabbatar da hakan ga gidan Talabijin na Channels Tv ta wayar tarho.

A cewarsa, bayan yan bindigar sunje garin, sun fara harbe-harben bindigogi a sama domin firgita mutane, inda kuma suka fasa shagunan mutane tare da Sace Dabbobin gida masu tarin yawa mallakin mutanen garin.

SP Gambo Isah, ya ce hadin gwiwar Sojin Kasa da yan sanda da kuma sojin sama suna kokarin ganin cewa sun kamo yan bindigar da suka kai harin.

Kazalika, ya ce tuni aka kai mutanen da suka ji raunika zuwa Asibiti domin kulawa da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: