An kama wani mutum bayan da aka kashe mutane hudu a wani harin bindiga da wuka da ba a saba gani ba a kasar Japan.
Wanda ake zargi da kai harin ya daba wa wata mata wuka tare da harbe wasu ‘yan sanda biyu da bindigar farauta a yankin Nagano.
‘Yan sanda sun bayyana sunan wanda ake zargin da Masanori Aoki, mai shekaru 31, wanda da ne ga wani dan siyasa a yankin.
Ba kasafai ake samun harbe-harben bindiga ba a kasar Japan, duk da kisan da aka yi wa tsohon Firayim Minista Shinzo Abe a watan Yulin bara.
Harbin jami’an ‘yan sanda yafi wahalar aukuwar, inda aka samu aukuwar hakan na karshe cikin shekaru fiye da 30 da suka gabata