An kashe mutane biyar tare da kona gidaje a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan kasuwa da ‘yan achaba a birnin tarayya Abuja

0 69

Akalla mutane biyar ne aka ruwaito an kashe tare da kona gidaje a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan kasuwa da ‘yan achaba a unguwar Dei Dei da ke babban birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa manema labarai cewa, wani hatsarin da wani dan achaba ya yi, ya jawo tabarbarewar doka da oda a cikin al’umma.

Manema labarai ba za su iya tantance adadin mutanen da suka mutu ba amma daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya tabbatar da cewa an kona gidansa.

An ce ’yan kasuwar sun kai wa dan achabar hari ne, wanda suka zarga da yin sakaci da ya kai ga mutuwar fasinja.

Rahotanni sun ce abokan aikin dan achaban sun yi yunkurin kubutar da shi daga hannun maharan kuma lamarin ya ci tura.

Wani shaida, kuma ya nuna cewa an kai farmaki kan direban tirelar da ya murkushe fasinjan har lahira, inda wasu suka yi ta kokarin kare shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: