Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ta dakatar da Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris.

Takardar dakatarwar mai dauke da kwanan watan 18 ga watan Mayu tace dakatarwar ta zama tilas domin bayar da damar gudanar da cikakken bincike kan manyan zarge-zargen da ake masa.

Sawaba ta bayar da labarin cewa jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun kama Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris, bisa zargin almundahana da karkatar da kudade da yawansu ya kai Naira miliyan dubu 80.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar, hukumar ta tabbatar da bayanan sirrin da ta samu dake bayyana cewa Akanta Janar na tarayya ya wawure kudaden ne ta hanyar kwangiloli na bogi da sauran ayyukan da suka sabawa doka ta hanyar amfani da ‘yan uwa, iyalai da makusanta.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: