Mutum daya ya mutu yayin da wasu biyar ke karbar magani a zanga-zangar da wasu matasa suka yi a ofishin ‘yan sanda a wani gari a arewacin kasar Ghana

0 64

Mutum daya ya mutu yayin da wasu biyar ke karbar magani bayan da wasu matasa masu zanga-zanga suka kai farmaki ofishin ‘yan sanda a wani gari a arewacin kasar Ghana.

‘Yan sanda a cikin wata sanarwa da suka fitar a yau sun ce masu zanga-zangar sun kuma sako wasu mutane shida da ake zargi daga sashin ‘yan sanda a yayin rikicin.

Zanga-zangar ta jiya ta biyo bayan kisan wani matashi dan shekara 28 da ‘yan sanda suka yi a yayin wani samame da suka kai wa wadanda ake zargi da fashi da makami a yankin.

Wata majiya mai tushe da ta ambato wani jami’in asibitin ya ce wadanda suka jikkata a rikicin na karbar magani sakamakon harbin bindiga.

Jami’in ya ce majiyyaci daya na fama da harsashi makale a kirjinsa.

‘Yan sanda sun ce a halin yanzu an shawo kan lamarin, kuma an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a rikicin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: