Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane 9 tare da jikkata wasu 10 sakamakon fashewar iskar gas da ta afku a safiyar yau a Aba road, unguwar Sabon Gari a jihar Kano.

Jagoran hukumar NEMA reshen jihar Kano, Nuradeen Abdullahi, ya tabbatar wa manema labarai hakan yayin da yake bayar da karin haske kan fashewar bututun iskar gas a Kano a yammacin jiya.

Police confirm four dead in Kano gas explosion - Punch Newspapers

Ya kara da cewa babban daraktan hukumar ta NEMA Mustapha Habib yana wurin da lamarin ya faru.

Nuradeen Abdullahi ya kara da cewa aikin ceton wanda aka fara da misalin karfe 10 na safe kuma aka rufe a hukumance da misalin karfe 5:15 na yamma.

Don haka ya yi kira ga al’umma musamman mazauna yankin da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu tare da gargadi kan yada labaran karya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: