Tsohon gwamnan Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya tabbatar da fita daga APC zuwa jam’iyyar NNPP ta tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso.

Shekarau ya sanar da matakin ne a wani taron siyasa a gidansa. Ya ce ya sanar da APC a mazabarsa ya fice kuma yanzu ya yanki katin zama ɗan Jam’iyyar NNPP.

Wakilin BBC a Kano ya ce nan take Kwakwanso ya ba Shekarau takarar kujerarsa ta Sanata ƙarƙashin NNPP a zaɓen 2023.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: