An kashe wani jami’in hukumar KAROTA a jihar Kano a lokacin da yake kokarin tsayar da wata tirela

0 93

An kashe wani jami’in hukumar KAROTA a jihar Kano a lokacin da yake kokarin tsayar da wata tirela dake gudun da ya wuce misali.

Kakakin hukumar, Abubakar Nabulisi, ya gayawa manema labarai cewa lamarin ya auku a jiya da misalin karfe sha biyu saura kwata na rana a mahadar titin BUK dake birnin Kano.

Abubakar Nabulisi yace an kama direban tirelan da yake gudun kuma an kwace tirelar.

Abubakar Nabulisi ya bayyana mamacin da suna Zaharaddeen Isma’il, mazaunin unguwar Sagagi.

Yace an dauke gawarsa daga asibtin kwararru na Murtala Muhammad.

Kakakin hukumar yace an mika wanda ake zargi ga ‘yansanda domin bincike.

Abubakar Nabulisi ya roki masu ababen hawa da su kiyaye da dokokin tuki kasancewar babu direban da za a kama ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: