Babbar kotun jihar Jigawa dake zama a Gumel a yau ta wanke wasu mutane 3 da ake zargi da hada baki tare da aikata kisa a karamar hukumar Babura.

Wadanda ake zargin Audu Ibrahim da Ali Baso da Tambai Ali, an gurfanar da su a gaban kotun bisa zargin kashe wani mutum mai suna Saminu Sani.

An zarge su da lakadawa Saminu dan karen duka yayin takaddama bayan sun halarci wani bikin aure a rugar Yola Fulani dake kauyen Kaya a karamar hukumar Babura.

Lauya mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu uku kuma ya bayar da bayanai a matsayin hujjoji da rahoton asibiti domin tabbatar da zarginsa.

Da yake zartar da hukunci, mai shari’ah Abubakar Sambo, ya tabbatar da cewa hujjojin da aka gabatar basu gamsar da kotu cewa mutanen sun yi kisan kai ba.

A saboda haka Mai shari’ah Abubakar Sambo, ya wanke su tare da bayar da umarnin a sake su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: