Fiye da mutane 80 sun rasa rayukansu, tun bayan fara damuna a watan Yuli a kasar Sudan.

Mai magana da yawun hukumar kare fararen hula ta kasar ya ce fiye da mutane 67 sun samu raunuka.

Ambaliyar ruwan dai ta shafi larduna 14 cikin 18 na kasar, yayin da ta rusa gidaje dubu 30.

Kazalika gonaki da dama da gine-ginen gwamnati sun lalace.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ambaliyar ta shafi akalla mutane dubu 102 a dukkan sassan kasar.

A bara ne hukumomi a kasar ta Sudan suka ayyana dokar ta baci ta tsawon wata uku saboda ambaliyar ruwan da ta hallaka mutane 100 a shekarar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: