Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani almajiri dan shekara 16 wadanda aka samu gawarsa cikin daji a yankin karamar hukumar Kiyawa ta jihar.
Kakakin rundunar na jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, shine ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa, yace an cire daya daga cikin idanuwan almajirin.
Shiisu Adam yace malamin almajirin, Malam Mustafa na unguwar Abuja a garin Shuwarin dake karamar hukumar Kiyawa ne ya kai rahoto ga ‘yansanda.
Yayi bayanin cewa malamin ya kawo rahoton cewa daya daga cikin almajiransa mai suna Yusufa Mustapha mai shekaru 16, yaje dajin dake kusa domin samo itace da misalin karfe 8 na safe.
Shiisu Adam ya kara da cewa malamin yayi bayanin cewa mamacin, wanda bai dawo gida ba kamar yadda aka yi tsammani, an same shi kwance cikin jini kuma an cire idonsa daya.
A cewarsa, an kai almajirin zuwa babban asibitin Dutse inda likita ya tabbatar da mutuwarsa. Shiisu Adam ya kara da cewa ana cigaba da kokarin neman wadanda suka yi aika-aikar
- Comments
- Facebook Comments