Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa Sun Tsaurara Tsaro Domin Gudun Tada Husuma Yayin Zaben Cike Gibi
Rundunar yansanda ta yi bayanin cewa an tsaurara tsaro a jihar Jigawa ne domin dakile yunkurin tayar da zaune tsaye a zaben ciki gibi na yau.
A cewar kwamishinan ‘yansanda na jihar, Effiom Ekot, tsaurara tsaron bashi da alaka da fashewar wani abu a Dutse ranar Talata inda wani mutum guda ya samu rauni.
Effiom Ekot ya sanar da haka yayin wata ganawa da manema labarai a Dutse.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa wani abu ya fashe a titin Hakimi Street dake Dutse inda ya raunata wani dan kasuwa mai suna Friday Frayo.
Tun daga lokacin aka fara ganin sabbin wuraren duba ababen hawa na sojoji akan manyan titunan jihar.
Kwamishinan na ‘yansanda ya bayar da tabbacin cewa ana binciken fashewar, inda ya kara da cewa za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin kamar yadda doka ta tanadar.