An raba Naira Triliyan 1.57 a tsakanin gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hakumomi a Najeriya – FAAC

0 96

Kwamatin rabon arzikin kasa ya raba kudin da ya kai naira triliyan 1.57 tsakanin gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hakumomi a watan maris.

Cikin wata sanarwar bayan taro da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ofishin babban akawu na kasa Bawa Mokwa ya fitar yace an raba kudade ne a taron kwamatin na watan Afrilu da aka gudanar a Abuja.

Sanarwar bayan taron tace jumillar naira triliyan 1.57 sun hada da kudaden hariji na naira biliyan 931.32 da aka tattara, da kuma kudaden harajin kayyaki na VAT naira biliyan 593.75 da kudaden harajin bankuna naira biliyan 24.97.

Sanarwar tace jumilla gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 528.69, yayin da gwamnatocin jihohi suka rabauta da naira biliyan 530.44.

Rahotan yace kananan hakumomi sun samu naira biliyan 387.002 da kuma naira biliyan 132.61 (wato kashi 13 kenan na harajin albarkatun kasa) wanda aka rabawa jihohin da suka samar da harajin.

Leave a Reply