Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin kara girman filayen noman shinkafa a damina daga hekta dubu 200 zuwa dubu 500 nan da shekarar 2030.
Gwamna Namadi ya bayyana hakan ne a jawabinsa yayin kaddamar da shirin noman shinkafa na daminar bana, wanda aka gudanar a kauyen Jura, dake karamar hukumar Auyo.
Ya ce a karkashin sabon tsarin sauya fasalin harkar noma, gwamnatin jihar ta riga ta kara yawan noman shinkafa na damina daga kasa da hekta dubu 100 zuwa dubu 200 a zangon noman 2023/2024.
Gwamnan ya ce gwamnati za ta raba injinan ban ruwa dubu 20, masu amfani da hasken rana da man fetur, tare da ingantattun iren shinkafa, takin NPK da Urea, da magungunan kashe ciyawa da kwari, wanda za a biya bayan an girbe amfanin gona.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar na ba manoman damina rancen kudade mai sauki, inda ake basu rangwame da kaso 30, 20, da 10 bisa dari.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa sama da manoma dubu hamsin da takwas ne za su amfana da wannan tallafi a karkashin shirin.