An rantsar da sabbin manyan sakatarori guda 16 a jihar Ribas

0 171

Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, a ranar Talata ya rantsar da sabbin manyan sakatarori guda 16 a zauren majalisar zartarwa na gidan gwamnati da ke Fatakwal.

Gwamnan ya bukace su da su kasance masu jajircewa da wajen ganin sun taimaka wa gwamnatin sa wajen cika alkawuran da ta dauka, inda ya ce gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen inganta walwala da tsaron jama’a.

Fubara ya kuma bukace su da su tsaya tsayin daka wajen tunkarar duk wani kuskure a ma’aikatun su, tare da yin alkawarin yin abinda ya dace a yayin gudanarda ayukkansu. An kuma ba wa sabbin sakatarorin da aka rantsar motoci jim kadan bayan rantsarda su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: