An Rufe Gidajen Giya Da Mata Masu Zaman Kansu A Jigawa

0 78

Rundunar Hisbah ya jihar jigawa ta bada umarnin rufe dukkanin gidajen giya dana mata masu zaman kan su yayin watan Ramadan.
Kwamandan Hisbah na jihar, Ibrahim Dahiru shine ya bayyana haka jiya yayin wata ganawa da manema labarai.
Ya ce matakin wani bangare ne na kokarin rundanar na dakile munanan dabi’u a cikin watan Ramadan.
Ibrahim Dahiru ya kuma yi bayanin cewa hukumar ta kai samame gidajen mata masu zaman kan su da inda ake saida giya,
Amma dai kawo yanzu hukumar bata samu wani rahoto wani wuri da ake aikita badala ba.
Kwamandan Hisban yace rundunar su zata kai samamen gama gari domin kama wadanda sukayi kunnen uwar shegu da umarnin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: