Mun Samarwa Da Maniyyata Hajji Masauki Na Musamman A Makka

0 68

Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar jigawa, tace ta samarwa maniyyatan ta masauki na musamman a birnin Makka domin gudanar da aikin Hajji na wannan shekarar.
Babban sakataran hukumar Alh Ahmad Umar Labbo shine ya bayyana haka a wata ziyara da ya kai kasar Saudiya.
Ya kuma ce duk da karancin masauki a kasar Saudiya, hukumar ta samarwa maniyyatan jihar masauki mai kima.
Ahmad Umar Labbo, Yayi bayanin cewa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar a shirye yake ya bada dukkan goyan baya da hukumar ke bukata domin jin dadin maniyyatan ta.
Ya yi kira ga maniyyatan da suka ajiye kasa da naira miliyan biyu da dari biyar da su yi haka kafin a bayyana kudin aikin Hajji a hukumance domin baiwa hukumar damar yin isassun shirye-shirye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: