An Samar da Cibiyar Gwajin Korona A Arewa Maso Gabashin Nijeriya

0 80

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya ta samar da wajan gwajin kwayar cutar COVID-19  a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, domin kula da kuma kaucewa yaduwar ctar COVID-19  yankin arewa maso gabas.

Babban daraktan Asibitin, Farfesa Ahmad Ahidjo, shine ya bayar da tabbacin hakan ciki wata ganawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na kasa, a yau Alhamis a Maiduguri.

Farfesa Ahmad ya bayyana cewa, haka kuma Asibitin zai iya gwada wanda ake zargin yana dauke da kwayar cutar dake Borno, Yobe, Adamawa da wasu jihohin da ke makotaka da su.

Haka kuma ya kara da cewa asibitin ya dauki matakan kare yaduwar cutar, tare da kiyaye lafiyar maras lafiya, ma’aikata da kuma masu ziyara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: