Jigawa Ta Rungumi Tsarin koya Karatu daga Gida

0 127

An shawarci iyayen yara a Jihar nan su tabbatar yaransu na sauraron shirin koyarwar dalibai ta gidajen Radio Jigawa wanda ma’aikatar ilimi Kimiyya da fasaha ta Jiha ta bullo da shi.


Shugaban Hukumar ilimi matakin farko na Jiha, Alhaji Salisu Muhammad Birniwa wanda ya bada wannan shawara, ya ce an bullo da shirin ne domin cike gibin karatun dalibai sakamakon zama a gida saboda rufe makarantu da aka yi sakamakon cutar corona.

Ya jaddada muhimmancin shirin, musamman ga dalibai da suke ajin karshe na manyan makarantun sikandire wadanda zasu fuskanci jarrabawar NECO da WAEC.

Alhaji Salisu Muhammad don haka ya yabawa Gwamnatin Jiha bisa goyon baya da ta baiwa ma’aikatar ilimi wajen gudanar shirin a Radio Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: