An samu mutane 532 da aka tabbatar sun kamu da cutar kyanda a Najeriya, daga cikin mutane dubu 1 da 686 da ake zargin sun kamu da cutar, ciki har da mutane 124 da suka mutu.
An samu wadanda suka kamun a kananan hukumomi 81 cikin jihohi 22, ciki har da babban birnin tarayya daga ranar 1 ga watan Oktoba zuwa ranar 16 ga watan Afrilun bana.
Hakan yazo ne cikin rahoton halin da ake ciki kan cutar a Najeriya ya zuwa ranar 27 ga watan Afrilun bana, wanda hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar.
Rahoton ya nuna cewa maza ne kashi 57 cikin 100 na dukkanin wadanda suka kamu.
Mafiya yawan wadanda suka kamu yara ne wadanda shekarunsu ya kama daga 1 zuwa 15. Kamar yadda yazo a rahoton, kashi 75 cikin 100 na wadanda suka kamu a jihar Jigawa suke, kuma jihar na da iyaka da yankin Zinder a jamhuriyar Nijar, inda aka samu barkewar cutar ta kyanda tun daga watan Oktoban bara.