RANAR MA’AIKATA: NLC Tayi Kira A Kara Shekarun Aiki Ga Ma’aikatan Gwamnati Zuwa Shekaru 65

0 77

Kungiyar kwadago ta kasa, NLC, ta yi kiran a sake bibiyar shekarun ritayar ma’aikatan gwamnati da shekarun aiki ga dukkan ma’aikatan gwamnati zuwa shekaru 65.

Shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero, shine yayi kiran yayin bikin ranar ma’aikata ta bana da aka gudanar jiya a Abuja.

Joe Ajaero ya kuma yi kiran a sake bibiyar albashin dukkan ma’aikata domin rage tazarar dake tsakanin ma’aikatan dake bangarori daban-daban na aikin gwamnati.

Yace akwai bukatar a kara yawan shekarun aikin ga dukkan ma’aikata kamar yadda aka yiwa ma’aikatan wasu bangarorin aikin gwamnati a kasarnan.

Joe Ajaero yace kungiyar cikin shekaru ta bukaci gwamnatin tarayya tayi karin albashi amma har yanzu bata samu kulawar gwamnatin tarayya ba. Dangane da biyan kudin ritaya, shugaban na NLC yace a lokuta daban-daban shugabannin kungiyar sun mika matsalar ga gwamnati ba tare da samun wani martani mai kyau ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: