An samu sabbin mutane 203 da suka kamu da cutar corona a jihohin Najeriya

0 414

An samu sabbin mutane 203 da suka kamu da cutar corona a kasar nan, a jiya lahdi.

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ce ta bayyana haka, cikin alkaluman da fitar a daran jiya.

Haka kuma an samu mutuwar mutum daya a dalilin cutar.

Cikin sabbin bullar cutar da aka samu a jiya, jihar legas ce keda adadi mafi yawa da mutane 186 da suka kamu, kaso 70 cikin 100 na wadanda ta samu a kwanakin da suka gabata.

Cibiyar ta NCDC ta bayyana cewa da wannan sabbin adadi da aka samu guda 203, kari ne akan 123 da aka samu a ranar asabar ba tare da rasa rai ko daya.

A cewar cibiyar kawo yanzu kasar nan ta samu kimanin mutane 169,532 da suka kamu da cutar, yayinda aka sallami mutane 164,699 bayan sun warke.

Haka kuma an samu mutuwar mutane 2,127 da suka mutu sakamokon cutar tun bayan bullar ta a kasar nan.

Kawo yanzu anyiwa sama da mutane milyan 2.3 gwajin cutar, cikin mutane milyan 200 da ake da su a kasar.

Leave a Reply