Manoma milyan 2.2 ne zasu samu tallafin noma na Naira bilyan 12 daga Gwamnatin Tarayya

0 84

Kimanin manoma milyan 2.2 ne zasu samu tallafin noma na naira bilyan 12 da millyan uku daga gwamnatin tarayya nan da makonni masu zuwa.

Fadar shugaban kasa ta bayar da tabbacin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya riga da ya amince da ware naira bilyan 6 da milyan 15 domin tallafawa manoma milyan 1.2 na rukunin farko da zasu ci gajiyar shirin.

Mai taimakawa shugaban kasa na musamman a bangaran noma, Andrew Kwasari, ya bayyanawa majiyar mu cewa bankunan dake da alhakin kula da shirin, ya zuwa yanzu sun fitar da rukunin farko na wadanda zasu ci gajiyar shirin.

Ya bayyana cewa, manoma milyan 1.2 na rukunin farkon wadanda suka samu nasarar samun tallafin, zasu karbi kudadan su nan bada jimawa ba, haka kuma yace wasu rukunin na biyu na sama da manoma milyan daya suma zasu sake samun tallafin kudi na kimanin naira bilyan 6.15.

A yayinda aka tambayeshi yawan adadin manoman da zasu iya samun tallafin, ya bayyana cewa za’a bayar da tallafin ne rukuni-rukuni kuma ko wanne rukuni za’a bayar da kimanin naira bilyan 6.15 kowanne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: