Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa ta bada tabbacin bada isasshen tsaro a lokacin bukukuwan Babbar Sallah

0 78

Rundunar yansandan jihar Jigawa ta baiwa alummar jihar nan tabbacin bada isasshen tsaro a lokacin bukukuwan babbar sallah.


Kwamishinan yansanda na jihar CP Usman Sule Gomna ya bada tabbacin a wata sanarwa mai dauke dasa hannun kakakin rundunar ASP Lawan Shiisu.


Yace rundunar zata girke yansanda a muhimman wurare da suka hada da filayen Idi da wuraren wasan yara da sauran wuraren taruwar jama-a a dukkannin kananan hukumomin jihar nan 27 domin bada tsaro.


CP Usman Sule Gomna ya kara da cewar rundunar zata hada gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin yin aiki tare wajen bada tsaron lafiya da kuma dukiyoyin alummar jihar na a lokacin bukukunwa sallar da kuma bayan babbar sallar.


Daga karshe ya bukaci iyaye dasu cigaba da kula da tarbiyyar yayansu domin zama shugabanni na gari

Leave a Reply

%d bloggers like this: