Yadda ake gudanar da Sallar Layya ta shekarar 2021

0 334

Babbar sallar idi da aka fi sani da sallar layya, ana gudanar da ita aduk shekara kuma itace babbar sallar da musulmai ke gabatarwa a fadin duniya, ta hanyar yanka dabbobi da suka hada da raguna, shanu, Rakumi da tumaki.

Sallar layya itace babbar bikin kalandar musulunci, domin tunawa da yardar da Annabi Ibrahim yayi na sadaukar da dansa Isma’il wajan yin hadaya dashi domin cika umarnin Allah.

Majiyarmu ta tattauna da masu sayarwa da siyan dabbobi a jihar katsina, kuma da yawa daga cikin su sun koka da yanda farashin dabbobin yayi tashin gwauron zabi.

Malam Aliyu Matazu mai shekaru 65 da majiyarmu ta zanta dashi a kasuwar raguna ta Yarkutungu, ya bukaci gwamnatin jihar data saukakawa musulmi wahalar da suke fuskantar a wannan lokaci ta hanyar biyan ma’aikatan jihar albashi.

Haka kuma masu sayar da raguna a kasuwar Yanturaku a babban birnin jihar sun koka da karancin cinikin da ake samu.

Wani mai saida rago a kasuwar ya bayyana cewa raguna biyu kawai ya saida a rana, haka kuma ya bayyana cewa tashin farashin bai tsaya iyakan dabbobi ba harda sauran kayayyakin abinci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: