Jami’an yan sanda sun kashe sama da yan bindiga 10 a kauyan Kundu dake karamar hukumar Rafi a jihar Niger.

An kashe yan bindigar ne a hutun karshan mako a yayin wani sumame da rundunar takai.

Haka kuma an kashe jami’an yan sanda biyu a yayin musayar wuta da yan bindigar.

Mazauna yankin sun bayyana cewa yan bindigar sun addabi yankin amma  yanzu yan sanda sun dakatar da su.

Gwamnan jihar ta Niger, Abubakar Bello a jiya Lahdi ya ziyarci garin domin jajantawa jami’an yan sandan da kuma yabawa kokarin da sukayi.

Gwamnan ya bawa rundunar tabbacin cewa gwamnatin sa zata bayar da dukkannin goyon bayan da ya dace, domin taimaka musu wajan ganin jihar ta zauna lafiya.

Haka kuma ya kara da cewa gwamnatin jihar ta samar da tsare tsaren da suka dace domin tabbatar da tsaro a jihar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: