An sanya kananan yara dubu talatin da shida a makarantu bayan sun shafe wasu lokuta basa zuwa a fadin jihar Jigawa

0 75

An sanya Akalla kananan yara dubu talatin da shida a Makarantu bayan sun shafe wasu lokuta basa zuwa makarantu a fadin jihar Jigawa.

Daraktan tabbatar da ingancin aiki na hukumar ilimi a matakin farko ta jihar Jigawa, Malam Hamisu Iliya shine ya bayyana hakan a lokacin bikin yaye daliban kungiyoyin kare hakkin kananan yara na makarantar firamare da sikandiren kwana ta Kudai wanda kungiyar Save the Children reshen jihar Jigawa ta shirya.

A cewarsa, an samar da cibiyoyin koyar da ilimin manya dari tara da ashirin, inda kuma ake baiwa dalibai mata kayan makaranta kyauta karkashin shirin bada ilimi ga kowa da yake samun tallafi daga bankin duniya.

Ya ce ilimin ‘yaya mata kyauta ne a jihar nan, inda ya bukaci iyayen yara su yi amfani da wannan damar wajen sanya yayansu a makarantu domin cin gajiyar shirin.

A jawabin da ta gabatar, shugabar makarantar kwana ta Kudai, Hajiya Aisha Abubakar ta yaba da kwazon daliban, inda ta bukace su da su kasance jakadun makarantar nagari a makarantun da za su je nan gaba domin ci gaba da neman ilimi.

Ta bukaci daliban su ci gaba da amfani da ilimin da suka samu a kungiyoyin daliban domin fadakar da al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: