Akalla mutane 6 ne rahotanni suka ce an kashe yayin da aka yi garkuwa da wasu da dama a jihar Katsina

0 132

Akalla mutane 6 ne rahotanni suka ce an kashe yayin da aka yi garkuwa da wasu da dama, bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a yammacin shekaranjiya Lahadi a kauyen Unguwar Samanja da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Mazaunan garin Daudawa dake makotaka, sun shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun isa kauyen ne da misalin karfe 5 da mintuna 49 na asuba, a lokacin da mazauna garin ke shirin Sallar Asubahi.

Karamar hukumar Faskari ta sha fama da hare-hare da dama daga ‘yan bindiga kuma tana daya daga cikin kananan hukumomi 13 na jihar Katsina da aka katse hanyoyin sadarwa.

Wata kungiyar farar hula a garin Daudawa ta yi kukan cewa duk da matakan tsaro da gwamnatin jihar ta dauka, har yanzu ana kai hare-hare a karamar hukumar ta Faskari.

Nasir Hassan, wani mazaunin garin Daudawa ya ce maharan sun shiga kauyen ne a kan babura mintuna kadan kafin sallar Asubahi kuma suka fara harbe-harbe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: