Bayan sanarwar kafa Kwamitin Kidaya, wato CENSUS, wanda aka kaddamar a ranar Laraba, an samu suka daga wasu sassa na al’umma game da yadda aka tsara kwamitin.
Kwamitin, wanda Ministan Tsare-Tsare da Tsarin Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, ke jagoranta, yana dauke da mambobi takwas, guda biyar daga yankin Kudu maso Yamma.
An bayyana cewa kwamitin zai duba hanyoyin samar da kudade da tsare-tsaren da za a bi domin gudanar da kidayar, wadda za’ayi a fadin kasar baki daya.
Wasu masu ruwa da tsaki sun nuna damuwarsu kan yadda kwamitin ya fi mayar da hankali kan yankin da shugaban kasa ya fito, suna ganin cewa wannan yana iya jefa kasa cikin rikice-rikice na rashin hadin kai, musamman ganin cewa yankuna kamar Kudu maso Gabas, Arewa maso Gabas da Kudu maso Kudu ba su da wakilci a kwamitin.