Nan da wata 6 yankin Arewacin Najeriya zai fitar da matsayarsa kan zaben 2027 – Hakeem Baba Ahmad

0 404

Muhawara ta sake kaurewa a Najeriya kan rawar da yankin arewacin ƙasar zai taka a babban zaɓe mai zuwa na shekara 2027, yayin da ‘yansiyasar yankin ke ganin sai da goyon bayansu ɗantakara zai yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa.

Hakan na zuwa ne bayan tsohon taimaka wa shugaban ƙasar a fannin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed ya yi wata hira, inda yake cewa nan da wata shida yankin zai fitar da matsayarsa.

Duk da cewa Hakeem ba shi ne mai magana da yawun al’ummar yankin ba, amma ana kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin manya a yankin, saboda tsohon matsayinsa na mai magana da yawun ƙungiyar dattawan yankin ta Northern Elders Forum (NEF).

Kodayake bai faɗa da bakinsa ba, ana ganin ya ajiye muƙamin nasa na gwamnatin Bola Tinubu ta jam’iyyar APC ne domin yin adawa da gwamnatin.

Tsarin siyasar Najeriya ya sa dole ne kowane ɗantakara ya karaɗe lungu da saƙo kafin ya iya samun ƙuri’un da yake buƙata.

Masana harkokin siyasa a ƙasar na ganin kalaman na Hakeem da ire-irensa na kan hanya amma idan aka cika sharaɗi ɗaya.

Leave a Reply