An yiwa Fursononi dubu 1300 afuwa a Kasar Burundi

0 88

Kasar Burundi ta yiwa Fursononi dubu 1,300 afuwa, a wani mataki da shugaban Kasar ya dauka na rage cunkoso a gidajen Fursunoni, a cewar Ministan Shari’a na Kasar.

Kimanin Fursunoni dubu 1,000 ne aka saka a fursunan Bujumbura, a wani taro da shugaban Kasa Evariste Ndayishimiye, da Ministocinsa da kuma Jakadun kasashen waje suka halarta.

Haka kuma an sake sakin wasu fursunoni 331 a birnin Gitega, wanda suka daga cikin Fursononi dubu 3,000 da gwamnatin tarayya ta yiwa Alkawarin sakin su.

Nan da sati biyu masu zuwa ne ake saran sakin karin wasu Fursunoni dubu 2,000 domin komawa ga iyalansu.

A watan Maris din da ya gabata ne gwamnatin kasar tayi Alkawarin sakin Fursunoni dubu 5,255, kimanin kaso 40 kenan.

Kungiyoyin Fararen hula sun bayyana cewa kimanin mutane dubu 13,200 ne ake tsare da su a gidajen Daurarrun.

Leave a Reply

%d bloggers like this: