An harbe wani mutum a Moundou a gabashin Chadi a cewar kafafen yada labarai dai-dai lokacin da jama’ar kasar ke ta zanga-zanga kan mulkin soji a kasar.

Wata mata ma ta mutu a babban birnin ƙasar, N’Djamena, kamar yadda aka rawaito lauyan gwamnati na cewa.

A cewar lauyan, Youssouf Tom, matar na cikin motar bas da masu zanga-zangar suka farwa.

Ɓangaren hamayya sun kira zanga-zangar duk da haramcin da sojin ƙasar da ke mulki suka sa.

Rahton BBCHausa

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: