Jihar West Virginia da ke Amurka, za ta bai wa matasa tukwicin dalar Amurka kwatankwacin naira dubu arba’in idan suka amince aka yi musu rigakafin cutar Coronavirus.

Rahoton da sashen Hausa na BBC ya wallafa ya nuna cewa, wannan jiha za ta bayar da tukwicin ne ga ’yan shekara 16 zuwa 35 da zummar basu kwarin gwiwar karbar rigakafin.

Gwamnan Jihar, Jim Justice, ya ce bisa la’akari da fargaba a kan yadda matasa ke juya wa rigakafin baya, ya sanya suka yanke wannan hukunci saboda muhimmiyar rawar gani da matasa za su taka a fagen yaki da annobar Coronavirus.

Kazalika, ya ce za’a bayar da wannan kudi har ga wadanda tuni aka yi musu rigakafin da ke rukunin shekarun haihuwa daga 16 zuwa 35.

Jihar West Virgina na daya daga cikin jihohin Amurka da aka shirya yi wa jama’a da yawa allurer rigakafin, sai dai lamarin ya fuskanci tasgaro a baya bayan nan saboda yadda matasa suka ki amincewa da ita.

Kamar yadda alkaluman jaridar New York Times suka nuna, West Virginia ce jiha mafi yawan masu cutar Coronavirus a duk fadin Amurka.

A halin yanzu dai an yi wa kashi 52 cikin 100 na mutanen jihar sun karbi allurer sau daya a cewa Gwamna Justice, inda ya nuna damuwa kan cewa wasu kashi 40 na iya yin baya-baya wajen zuwa a yi musu rigakafin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: