Za a yiwa yara 109,560 riga kafin Polio ta hanyar sayo bada alawa a Guri da Kirikasamma

0 235

Majalisun Kananan Hukumomin Guri da Kirikasamma na nan Jihar Jigawa suna kokarin ganin cewa an yiwa Yara dubu 109,560 Riga kafin Polio ta hanyar sayo Katan din Alawoyi domin rabawa kananan yaran da za a yiwa rigakafin.

Jami’in Yada Labarai na Kananan Hukumomin 2, Malam Sunusi Doro, shine ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a birnin Dutse.

Malam Sunusi Doro, ya ce kimanin Kananan Yara dubu 61,560 ne ake saran yiwa rigakafin a Kirikasamma, inda kuma za’a yiwa Yara dubu 48,000 a karamar hukumar Guri.   

Jami’in Yada Labaran Yankunan ya ce Kananan hukumomin sun karbi Isassun rigakafin da zasu wadatar dasu a lokacin aikin.

Kimanin Kwanaki 5 ne ake saran za’a kwashe ana yin rigakafin wanda aka fara tun daga ranar 18 ga watan Satumba a kanana hukumomi 27 na fadin Jihar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: