Ana Hasashen Fintiri Zai Sauya Sheƙa Yayin da Kakakin Majalisar Adamawa da ‘Yan Majalisa 13 Suka Fice Daga PDP
Rahotanni daga jihar Adamawa na nuna cewa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Bathiya Wesley, tare da wasu ‘yan majalisa 13 sun ajiye jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a wani mataki da ake dangantawa da shirin sauya sheƙar gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri.
Majiyoyi sun ce ficewar ‘yan majalisar daga PDP na da nufin share fagen sauya sheƙar gwamnan zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), bayan alamun da ya nuna a baya-bayan nan na yiwuwar komawa jam’iyyar.
An ruwaito cewa Fintiri ya samu saɓani da wasu gwamnonin PDP a taron jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan, jihar Oyo, lamarin da ya ƙara haifar da hasashen sauya sheƙarsa.
Haka kuma, a ziyarar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai Adamawa domin ƙaddamar da wasu ayyuka, an ce sun yi tattaunawar siyasa da gwamnan, abin da ya ƙara janyo ce-ce-ku-ce.
Idan har Fintiri ya sauya sheƙa zuwa APC, hakan zai ƙara yawan jihohin da jam’iyyar ke iko da su zuwa 30, yayin da PDP za ta rage da gwamnonin jihohi uku kacal, a cewar rahotannin.
Kakakin Majalisar ne ya sanar da murabus ɗin nasu a zauren majalisa yayin zaman majalisar na jiya. Daga cikin waɗanda suka fice har da mataimakin kakakin majalisa da wasu ‘yan majalisa daga mazaɓu daban-daban a faɗin jihar.
Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar, Mahmud Kallamu, ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan majalisar na ci gaba da tuntubar al’ummominsu kafin su bayyana sabuwar jam’iyyar da za su koma, yana mai cewa matakin gwamnan zai taimaka wajen tantance matakin da za su ɗauka.
A nasa ɓangaren, jami’in hulɗa da jama’a na APC a jihar, Mohammed Abdullahi, ya ce abin da ke faruwa na nuna yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ke jan hankalin ‘yan adawa zuwa jam’iyya mai mulki.