“Ana kaiwa Gidajen gyaran halayya hare-hare domin a kunyata gwamnatin tarayya” a cewar Ministan Harkokin Gida

0 91

Ministan Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida Mista Rauf Aregbesola ya bayyana cewa ana kaiwa Gidajen gyaran halayya hare-hare domin a kunyata gwamnatin tarayya.

A cikin yan watannin nan akan yawan kaiwa gidajen gyaran halayya hare-haren inda aka saki daurarru tare da kashe Jami’an tsaro.

Hari na baya-bayan nan shine wanda aka kai ranar Juma’a a gidan gyaran halayya na Abologo ta Jihar Oyo, wanda wasu yan bindiga suka kai.

Da yake jawabi a Jiya lokacin da yake duba gidan gyaran halayyar Ministan ya ce gwamnati zata hukunta wanda suka kai harin.

A cewarsa, hare-haren da ake kaiwa gidajen gyaran halayyar shiryayyen abune wanda ake kitsawa domin bata gwamnati a Idon Jama’a.

Ya ce gwamnatin tarayya zata kamo masu kaiwa hare-haren harda kuma mutanen da suke tserewa daga gidajen.

Kazalika, ya ce tuni suka fara kama wadanda suka gudu daga gidajen, kuma zasu cigaba da kama sauran wadanda suka gudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: