Jakadan kasar China a Najeriya, Yu Dunhai, ya bayyana cewa ana kokarin kafa masana’antun kera motoci masu amfani da lantarki da sauran masana’antun kere-kere a Najeriya.
Mr. Dunhai ya bayyana hakan ne ga Ministan Ma’adanai, Dr. Dele Alake, a wani taron tattaunawar bangarorin biyu da aka gudanar baya bayan nan.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Minista kan harkokin yada labarai, Segun Tomori, ya fitar jiya a birnin Abuja.
A cewar Tomori, jakadan ya jaddada bukatar kara hadin gwiwa tsakanin Najeriya da kasar China domin amfani da damar da ke cikin bangaren ma’adanan Najeriya ta hanyar kafa masana’antun motoci masu amfani da lantarki.
Jakadan ya bayyana goyon bayan kasar China ga manufar Najeriya na kara darajar albarkatun cikin gida, inda ya nuna cewa daya daga cikin manyan manufofin Shugaban kasar China, Xi Jinping, shi ne bunkasa masana’antu a nahiyar Afirka.
Ya tunatara da cewa Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Xi Jinping sun gudanar da ganawar manyan shugabanni a ziyarar da Tinubu ya kai kasar China a baya-bayan nan domin cimma wannan manufa.