Anyi Garkuwa Da Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa

0 81

An yi garkuwa da tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa Farfesa Onje Gye-Wado.
Kakakin rundunar yan sandar jihar DSP Ramhan Nansel ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau.
Yace anyi awon gaba dashi a safiyar yau juma’a yayin da yan bindiga suka kutsa gidan dake kauyen Gwagi karamar hukumar Wamba.
Kakakin yan sandar jihar ya yace, yan sanda tare da sauran jami’an tsaro suna iya bakin kokarin wasu wajen kubutar da wanda aka sace ba tare da an cutar da shi.
Kwamishinan yan sandar jihar Nasarawa CP Maiyaki Baba ya bada tabbacin kubutar da wadanda aka sace musamman tsohon mataimakin gwamnan jihar Farfesa Onje-Gye-Wado.
Kazalika kwamishinan ya tura jami’an yan sanda da yan sakai da kuma mafarauta domin kubutar da wanda aka sace tare da kamo yan bindigar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: