Anyi sabon mukadashin sakataren zartarwa na asusun adashen gata na fansho a jihar Jigawa

0 84

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa ya amince da nadin Alhaji Kamilu Aliyu Musa a matsayin Mukadashin Sakataren Zartarwa na Asusun Adashen Gata na Fansho na Jiha da kuma Kananan Hukumomin Jihar Jigawa.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da da Shugaban Ma’aikata Alhaji Hussain Ali Kila ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Dutse.

Sanarwar tace nadin ya fara aiki nan take, biyo bayan yadda Gwamna Badaru Abubakar ya sauke Alhaji Hashim Ahmad Fagam, daga mukamin.

Haka kuma Sanarwar ta ce Kafin bashi wannan matsayin Alhaji Kamilu Aliyu Musa shine Mukaddashin Daraktan kudi na Asusun Adashen Gata na Fansho na Jiha.

Kazalika Sanarwar ta kara da cewar nadin ya biyo bayan cancantarsa da kuma kwarewarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: