Mata sun fito zanga-zangar nuna adawa da kin jinin jagorancin kungiyar Taliban

0 98

Wasu gomman mata sun fito zanga-zangar nuna adawa da kin jinin jagorancin kungiyar Taliban a Kabul babban birnin kasar Afghanistan da kuma lardin Badakhshan da ke arewa maso gabashin kasar.

Matan na kuma nuna bacin ransu kan rashin ganin sunan wata mace ko da guda daya a kunshin sabuwar gwamnatin kasar da aka sanar.

Wasu rahotanni na cewa dakarun na Taliban sun yi wa matan duka kafin tarwatsa su.

Wata kafar yada labarai ta ce an tsare wasu daga cikin ‘yan jaridar da ke mata aiki na wani lokaci, kuma an dake su saboda sun dauki rahotannin abubuwan da su ka faru a wajen zanga-zangar.

Kungiyar wadda kawo yanzu ba ta mayar da martani kan batutuwan da matan ke bore a kai ba, ta ce ba za ta lamunci a ci gaba da yi ma ta zanga-zanga irin wannan ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: