APC ta cikawa yan Najeriya alkawarin da ta dauka – Abdullahi Adamu

0 62

Shugaban Jam’iyar APC ta Kasa Sanata Abdullahi Adamu, ya ce Jam’iyar APC ta cikawa yan Najeriya Alkawarin da ta dauka.

Sanata Adamu, ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyar APC a Jos babban birnin Jihar Filato.

Shugaban, ya ce Jam’iyar ta samu tagomashi ganin yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya halarci taron kaddamar da Dan Takarar, wanda hakan ya ke nuni da irin Jajircewar sa wajen ganin cewa yan Takarar Jam’iyar sun kai ga Nasara.

Abdullahi Adamu, ya ce nasarorin da Gwamnatin Shugaba Buhari, ta samu ya wuce na mutanen da suka Shugabanci kasar nan ta fannin Manyan Ayyuka da sauran su.

Haka kuma, ya ce Bola Tinubu, shine mutumin da ya cancanci a zaba a shekarar 2023, domin Dorawa akan wasu aikace-aikacen da Gwamnatin Shugaba Buhari ta aiwatar.

Shima a Jawabinsa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce Jam’iyar APC a shirye take ta marawa Tinubu baya domin ya kai ga nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: