Dakarun sojin saman Najeriya sun ƙaddamar da hare-hare kan wasu sansanonin ‘yan fashin daji a jihar Kaduna

0 85

Dakarun sojin saman Najeriya sun ƙaddamar da hare-hare kan wasu sansanonin ‘yan fashin daji a wasu yankunan ƙananan hukumomin jihar Kaduna, tare da kashe ‘yan fashin daji masu yawa.

A wata sanarwa da kwamishinan al’umuran tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan a fitar.

Ya ce an kai hare-hare kan wasu sansanonin ‘yan fashin daji a wasu ƙauyuka da ke yankin ƙaramar hukumar Igabi.

Ya ƙara da cewa a lokacin wannan hari an samu nasarar kashe ‘yan fashin daji uku tare da kubutar da wasu da aka yi garkuwa da su a sansanin’

Haka kuma ya ce dakarun sojin saman sun hangi wasu ‘yan fashin dajin a wani waje mai nisan kilomita hudu a arewa maso yammacin Godani, inda anan ne ake ta kashe Yan bindigar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: