Gwamnatin jihar Borno ta ce akwai yara miliyan 1.8 da ba sa zuwa makaranta a jihar

0 93

Gwamnatin jihar Borno ta ce akwai yara miliyan 1.8 da ba sa zuwa makaranta a jihar, inda ta bayyana hakan a matsayin abin damuwa.

Kwamishinan ilimi mai zurfi Abba Wakibe ne ya bayyana haka a lokacin bude taron horas da matasa 968 na shirin bayar da horon Yara marasa galihu a jihar Borno da aka gudanar jiya a Maiduguri.

Ya kuma jaddada cewa tashe-tashen hankula sun yi tasiri sosai a wajen dakile fannin ilimi, wanda hakan ya sanya yaran yin aikatau.

Shugabar shirin, Hajiya Inna Galadima, ta ce an zabo malamai 968 a fadin kananan hukumomin jihar 27, wadanda za’a bawa horo na tsawon makwanni uku domin horar da yaran a jihar.

Ta ce shirin zai yi matukar rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: