‘Ya’yan jam’iyyar PDP za su hada kai domin samun nasarar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2023 – Bukola Saraki

0 103

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya ce ‘ya’yan jam’iyyar PDP za su hada kai domin samun nasarar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2023.

2023: PDP crisis 'll be resolved soon - Saraki

Tsohon dan majalisar ya bayyana haka ne jiya a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, yayin da yake zantawa da manema labarai a wajen wani taron addu’o’in tunawa da mahaifinsa, Olusola Saraki jiya shekara 10 kenan.

A makwannin da suka gabata dai an yi ta cece-ku-ce a cikin jam’iyyar PDP, akan kiran da Nyesom Wike, gwamnan Rivers da abokansa suka na tilastawa Iyorchia Ayu akan yayi murabus a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Kiran murabus din Ayu ya biyo bayan yanda dan takarar shugaban kasa da kuma shugaban jam’iyyar na kasa suka fito daga yanki daya ne.

Da yake magana jiya a Ilorin, Saraki ya ce warware rikicin zai baiwa yan kasarnan mamaki wajen lashe zaben 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: