Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa a yau yawan al’ummar duniya ya cika miliyan dubu takwas

0 97

Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa a yau yawan al’ummar duniya ya cika miliyan dubu takwas.

Haka zalika majalissar ta bayyana cewa yawan adadin al’ummar kasarnan ya kai Miliyan 216, hakan na nufin kasarnan tana da kaso 2.7 na adadin al’ummar duniya baki daya.

Majalisar ta bayyana hakan ne a yau Talata a cigaba da bakin tunawa da Ranar Yawan Al’umma ta duniya.

Rahoton ya ce sama da rabin al’ummar nan sunfito ne daga kasashen 8 na duniya ne.

Kasashen sun da suka hada da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Masar, Habasha, Indiya, Najeriya, Pakistan, Philippines da Jamhuriyar Tanzaniya.

Rahoton ya kara da cewa Indiya za ta wuce kasar China a matsayin kasa mafi yawan jama’a a duniya a 2023.

Rahoton ya kuma bayyana cewa yawan haihuwa ya ragu matuka a shekarun baya, bayan nan a kasashe da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: